Home | English | Hausa | Books | Reviews | Readers | News | Articles | Awards | About | Contact | Download | Audio/Video

Book Reviews_Hausa

mudplaster-house.gif
savannah.jpg
mud-house_115.gif
people_120.jpg
books2_150.jpg

Nazari Da Tsakure Daga Littafin Xankutungayya (Da Wasu Labarai)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

 

Sunan Littafi: Xankutungayya (Da Wasu Labarai).

Marubuci: Bukar Usman.

Mawallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano.

Shekarar Wallafa: 2005.

Yawan Shafuka: 70.

Farashi: Ba a faxa ba.

 

Littafin Xankutungayya (Da Wasu Labarai), kamar sauran guda biyar da muka yi wa sharhi a makonnin da suka gabata, shi ma yana xauke ne da tatsuniyoyi masu nishaxantarwa, ilimantarwa da kaifafa tunani. Haka kuma, littafin, xaya ne daga cikin jerin littattafai guda shida irinsa da marubucin ya rubuta a tsarin littattafan Taskar Tatsuniyoyi.

Kafin mu tsakuro xaya daga cikin tatsuniyoyi goma sha biyu da ke cikin littafin nan, ya zama wajibi mu xan kawo bayani kaxan game da marucin littafin, domin kuwa Hausawa ma sun ce, a san mutum a san cinikinsa, ko kasuwa a san dillali...

An haifi Dokta Bukar Usman ne a garin Biu na Jihar Borno, a ranar 10 ga watan Disamba na shekarar 1942. Bayan ya yi makarantar firamare a Biu, ya je Maiduguri inda ya yi karatun sakandare, kafin ya je King's College da ke Legas, inda ya yi karatun share fagen shiga jami'a. Daga nan ya shiga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digiri a fannin Dubarun Al'amuran Mulki Da Hulxa Da Qasashen Waje a shekarar 1969.

Bayan Dokta Bukar Usman ya kammala karatun jami'a, sai ya kama aiki da Gwamnatin Tarayya, inda har ya kai muqamin Babban Sakatare a Ofishin Shugaban Qasa. Ya yi ritaya daga aikin gwamnati a shekarar 1999, inda saboda gamsuwa da aikinsa har Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar yabo ta qasa ta OON a shekarar 2000.

Dokta Bukar Usman dai ya yi rubuce-rubuce da dama, mafi yawansu ma a cikin harshen Turanci, amma bayan ya yi ritaya ne ya tsunduma sosai cikin harkar rubuce-rubuce, inda har ya yi bincike ya rubuta waxannan littattafai guda shida na Taskar Tatsuniyoyi. Magidanci ne shi da ke zaune tare da iyalinsa a birnin Abuja.

Dayake za mu yi tsakure ne daga cikin littafin nan, za mu xauki fitattar tatsuniyar nan ce ta Xankutungayya, wacce da ita ne aka yi amfani wajen sanya wa littafin suna. Tatsuniyar dai ta fito ne a cikin littafin daga shafi na 5 zuwa na 14. Idan mun shirya, ga tatsuniyar Xankutungayya:

Ga ta nan, ga ta nanku:

Akwai wani mutum da ke zaune a wani gari mai suna Raqumawa tare da matarsa da 'ya'yansu su goma sha xaya. Rannan sai matarsa ta haifi xa namiji, ya zama na goma sha biyu. Da haihuwar yaro kuwa sai ya yi magana, ya ce wa uwarsa: "Kada ma a yi wahalar raxa mini suna, domin sunana Xankutungayya." Ya qara da cewa, ragon sunansa ma kada a yanka, a bar masa ya rinqa hawa. Iyayen suka yi haka, jama'ar gari suna ta mamakin wannan yaro da abubuwan da ya yi.

Ana nan, ana nan, sai wata rana yayyen Xankutungayya suka shirya za su gidan wata mata da suka saba zuwa gidanta hira da 'ya'yanta su goma sha biyu. Sai Xankutungayya ya ce zai bi su amma babban wansu ya hana shi bin su. Amma ya bari sai da yayyen suka tafi, sai ya bi su a baya. Da isar su gidan, sai matar ta yi musu maraba; ta yi musu shimfixa, suka zauna; ta kawo musu abinci mai daxi suka ci, suka fara hira. Amma fa duk zuwan da suke yi gidan, ba su san cewa matar nan Dodanniya ce ba.

Suka zauna suna ta hira kamar yadda suka saba kullum. Kuma duk sadda suka yi barci a gidan, Dodanniyar kan tashe su, su tafi gida. Ashe duk wannan dabara ce take yi don su saki jiki da ita, wata rana ta cinye su. Kuma tuni ta yi tanadin manyan tukwanen dafa su, ta sha romo. To, a daren da suka je tare da Xankutungayya ma, duk sauran sun yi barci in ban da shi. Can cikin dare sai ya ji ana wasa wuqa, sai ya ce a ransa: "A'a, lafiya kuwa?" Sai ya kwanta ya yi kamar yana barci. Da aka xan jima sai ya ga Dodanniya tana sanxa, har ta shiga wajen yara. Da ya ga lallai ta nufi yayyensa, sai ya yi tari da qarfi. Da ta ji tarinsa, sai ta koma da sauri. Da aka jima, sai ta sake dawowa; shi kuwa Xankutungayya ya qara yin tari, ta koma.

A zuwanta na uku ne fa da ta ji tarin Xankutungayya, sai ta voye wuqa ta leqo ta ce: "Kai xan samari ba ka barci ne?"

Sai ya ce: "Ai ni ba na barci in ba a kan rairayin qorama mai sanyi ba."

Da ta ji haka, sai ta xauki masaki ta tafi neman rairayin qorama. Kafin ta dawo sai Xankutungayya ya fito da wata 'yar batta, ya buxe bakinta, ya zazzago wani magani, ya matsa kusa da wutar da ta hura, ya barbaxa maganin nan a cikin wutar, sai wani hayaqi ya tashi. Da 'ya'yan Dodanniya da yayyensa suka shaqi wannan hayaqi, sai barcin da suke yi ya qara nauyi.

Nan da nan Xankutungayya a cikin sauri irin na hatsabiban mutane ya bi ya tuve wa 'ya'yan Dodanniya kayan jikinsu, ya sanya wa yayyensa. Kuma ya tuve wa yayyensa nasu kayan, ya sanya wa 'ya'yan Dodanniya. Da ya gama wannan aiki sarai, sai ya kwanta, ya shiga jira. Can sai Dodanniya ta dawo, ta kawo rairayi ta ba Xankutungayya. Sai ya ce: "Yawwa Iya, na gode. Yanzu zan yi barci."

Da aka jima sai Dodanniya ta dawo da wata sharveviyar wuqarta a hannu, ta iske Xankutungayya ya yi barci. Nan da nan cikin gaggawa da qeta ta bi duk 'ya'yanta ta yanke, tana zaton samarin da sukan je hira gidanta ne. Amma ba ta yanka Xankutungayya ba saboda ta ga shi qarami ne. Ta qyale shi, da nufin kiwata shi ya yi qiba.

Da Dodanniya ta fita za ta fara shirin kwashe naman da take zato ta samu, sai Xankutungayya ya zaro battar nan tasa ya sake barbaxa garin maganin nasa a kan wuta. Kafin qifta ido, hayaqi ya murtuke xaki. Cikin gaggawa ya tashi yayyensa, ya gaya musu abin da ya faru, kuma ya ce su yi maza-maza su gudu gida. Ya ce shi zai bi su da gari ya waye, kada su jira shi. Take suka sulale, suka gudu.

Da gari ya waye, sai Dodanniya ta zo za ta fara tattara waxanda ta yanka, a zatonta 'yan uwan Xankutungayya ne. Yana ganin ta sai ya kaxa battarsa, sai ga ragonsa ya zo ya harari Dodanniya, yana yi mata kallon raini ya ce: "To, waxannan fa 'ya'yanki ne kika yanka, ba 'yan uwana ba."

Da ta lura da haka, sai ranta ya vaci ta yi wani qaraji, ta yi wuf ta kai masa bara za ta cafke shi, sai ya bauxe. Ta sake rarumo shi, amma sai ya xare bayan ragonsa. Rago kuwa kamar ya san zancen, sai ya kama sukuwa kamar walqiya, ya tsere mata fintinkau, ya bar ta sororo a cikin baqin ciki.

Dodanniya ta xauko xan magurjinta na tsafi, ta bi 'ya'yanta tana buga wa kowannensu a ka. Nan da nan namansu ya zama na tumakai, ta soye suka cinye ita da autarta. Daga nan ta yi alqawari sai ta rama qetar da Xankutungayya ya yi mata.

Bayan 'yan kwanaki, sai Dodanniya ta je bakin garin su Xankutungayya ta rikixe ta zama kanya kuma ta kwaza 'ya'ya da yawa, har sun kusa nuna. Da yaran gari suka ga kanyar sai suka yi murna. Da ta nuna, sai wasu daga cikinsu suka dinga kaxo 'ya'yan suna sha. Har dai wata rana yara da yawa suka hau kanta suna xiba. Da Dodanniya ta ga haka sai ta tashi sama da su, ba ta tsaya ba sai a gidanta. Nan da nan ta gaya wa autarta cewa nama ya samu. Sai ta umurce ta da ta wanke tukwane. Tana kuwa  cikin wanke tukwane sai Xankutungayya ya ji labarin abin da ya faru, sai ya rikixa, ya zama xan maraqi, ya je gidan Dodanniya. Da zuwansa sai ya fara cin shuke-shuken da ke gidan, watau dai yana yi mata varna. Yana cikin wannan varna sai Dodanniya ta ce wa yaran da ta sato, su je su kori xan maraqin mai yi mata varna.

Da ya ga sun doshe shi sai ya qi gudu, amma da suka zo dab da shi, sai ya xan gudu ya xan matsa gaba kaxan kuma ya ci gaba da varna. Yara kuma suka xan matsa kusa da shi, ya xan qara gaba kaxan. Haka dai ya dinga jan su, har sai da suka yi wa Dodanniya nisa. Sai ya rikixa ya zama mutum, ya ce da yaran nan su hanzarta su gudu. Ya jaddada musu cewa idan ba su gudu ba, Dodanniya za ta cinye su. Da suka ji haka, sai suka sheqa da gudu, suka koma garinsu, suka gaya wa iyayensu abin da ya faru.

Shi kuwa Xankutungayya sai ya hau ragonsa, ya koma gidan Dodanniya. Da ya tabbatar ta gan shi, sai ya yi mata gwalo ya ce mata: "Na kuvutar da yara daga sharrinki, sun koma wurin iyayensu. Ni ne Xankutungayya na yi miki gayyar tawa, wadda ba za ki iya ramawa ba har abada." Wannan abu da Xankutungayya ya yi wa Dodanniya da maganar da ya gaya mata, suka sa ta shiga tunani da qulla yadda za ta xauki fansa a kansa.

Ana nan sai Dodanniya ta rikixa, ta zama  mace kyakkyawar gaske, ta xauki wani adudu ta je cin kasuwa. Masoya suka yi ca a kanta, kowa yana so ya aure ta amma ta ce ba wanda za ta aura sai wanda ya buxe wannan adudun. Samari da yawa suka gwada amma duk suka kasa.

Bayan 'yan kwanaki, har samari sun fid da rai, sai xaya daga cikin yayyen Xankutungayya ya ji labari, ya bincika inda take a kasuwa ya je kuma ya gan ta, sai ya ji yana son ta. Ita kuma Dodanniya ta gane shi, saboda haka sai ta yi tsafi ta yadda idan ya gwada buxe adudun zai buxe. Da zuwansa kuma ya gwada sai adudun ya buxe, mutane suka yi ta mamaki, shi kuma ya yi murnar samun kyakkyawar mata. Aka xaura aure, ba ta jima ba ta tare a gidansa. Amma bayan 'yan kwanaki sai ta qwaqwale wa mijin ido xaya, ta tafi da shi ta bar shi da jinya.

Xankutungayya da jin wannan aika-aikar, ya tabbatar da cewa Dodanniya ce. Don haka ya quduri aniyar sai ya xauko fansar abin da ta yi wa yayansa. Sai ya rikixa ya zama Bafilatana, ya xauki nono, ya je gidanta talla. Da isar sa sai autar Dodanniya ta fito ta saya. Shi kuma ya yi mata araha. Kullum sai ya kai tallar nono, Dodanniya ba ta gane gogan ne ba. Da haka har Dodanniya ta saba da Bafilatana qwarai da gaske.

Wata rana sai Bafilatana, watau Xankutungayya ya zo gidan Dodanniya a fusace. Dodanniya ta tambayi Bafilatana dalilin fushinta, sai ta ce: "Wani mutum wai shi Xankumale yake zuwa yana kashe mana shanu. Ga shi yanzu duk sun kusa qarewa."

Dodanniya ta ce: "Ke ba sunansa Xankumale ba, sunansa Xankutungayya. Mugun mutum ne. Ba shanunku kaxai ba, ku kanku ma ku yi hankali da shi. Ni 'ya'yana goma sha xaya ya sa na kashe. Kwanan nan ma na kusa makantar da xan uwansa. Kin ga idon yayansa da na qwaqule."

Sai Bafilatana ta ce: "Tir da ganin idon lalatacce."

Sai Dodanniya ta ce: "Yau saura kwana uku ma in ba kyanwata idon mugun ta cinye."

Bafilatana ta ce: "Kash, da idon nan zai yi wa qanena daidai da kin ba ni shi. Shekaranjiya saniya ta harbi idonsa xaya ya fashe ya tsiyaye."

Cikin xoki da qeta Dodanniya ta ce: "Af, don wannan ai sai in ba ki."

Da jin haka sai Bafilatana ta yi farat ta ce: "Ai ko na gode."

Dodanniya ta qara yiwa Bafilatana gwaninta, sai ta gaya mata yadda za ta sa masa idon, ta ce: "A nemo qwayayen kifi guda bakwai da hantar baqin kare da kiyashi guda bakwai da kaucin marke; a shanya su bushe, sai a niqa, a rinqa sa masa a gurbin idon har kwana uku. A rana ta huxu sai a sa idon, zai zauna daram."

Bafilatana, watau Xankutungayya ta amshi ido, ta yi godiya. Da ta gusa kaxan sai ta tuve kayan Fulani, sai ga Xankutungayya ya bayyana. Sai ya yi wa Dodanniya gwalo ya ce: "Kin ga ni ne Xankutungayya." Sai ya yi wani hatsabibanci ya vata, Dodanniya ta daina ganinsa. Bai tsaya a ko'ina ba sai gida. Da ya isa ya yi yadda Dodanniya ta kwatanta masa, idon yayansa kuma ya zauna daram, kamar ba a tava qwaqule shi ba.

Rannan kuma sai Dodanniya ta rikixa ta zama kyanwa. Ta kama hanya ba ta tsaya ko'ina ba sai gidan su Xankutungayya. Da shigarta sai ta iske shi yana barci, sai ta lavava, har ta kai kusa da shimfixarsa. Sai ta yi wani karatu irin na tsafinta, ta tofa masa a fuska, sai ya zama vera, sai ta xauke shi ta kai gidanta, ta sa shi a quryar xaki. Daga nan ta yi masa wani tofin, ya koma mutum. Ita kuma ta rikixa ta zama mutum, sai ta harare shi, fuskarta murtuk, tana cike da fushi, ta ce: "Xankutungayya, yau fa ga ni ga ka, qaryarka ta qare." Xankutungayya bai tsorata ba kuma bai ce mata komai ba.

Can da Dodanniya ta xan huta sai ta sa autarta tsaron Xankutungayya; ita kuma ta kama hanyar kasuwa sayen kayan yaji wanda za ta dafa shi da shi. Tafiyarta ke da wuya sai Xankutungayya ya yi wa 'yar auta dabara, ya karve kayan jikinta ya sa, ita kuma ya sanya mata nasa. Can sai ya ji motsin Dodanniya ta dawo, ya zabura, ya tarye ta yana kwaikwayon maganar 'yar auta, yana yi mata maraba. Bayan wani xan lokaci kuma sai ga 'yar a cikin kayan Xankutungayya tana yi mata maraba. Sai Xankutungayya ya dubi Dodanniya ya ce mata: "Ga munafukin nan Xankutungayya yana nunawa wai shi ne ni 'yar autarki har da cewa, ‘Sannu da zuwa inna.' Yau dai qaryarsa ta qare."

Sai Dodanniya ta ce: "Lallai kam, bar ni da lalatacce!"

Nan take ta yi wuf ta shaqo 'yarta, ta sa wuqa ta yanka.

Tana gama yanka autarta sai Xankutungayya ya buga tsalle gefe, ya kwance zannuwan da ya xaura, ya dubi Dodanniyar nan ya ce: "'Yar auta kika yanka, ni ko ni ne Xankutungayya gwanin gayya. Na yi miki gayyar tawa!"

Yana gama faxa mata haka sai ya yi wal, ya vace. Dodanniya ta kama 'yarta ta tuve kayan jikinta, sai ta ga lallai kuwa autarta ce ta yanka. Nan take sai ta haxiyi zuciya ta mutu.

Qurunqus! Qarshen wannan tatsuniya ke nan, kuma tana xauke da darussa kamar haka: Qaunar juna da son 'yan uwa kan qara wa juna danqon zumunci, kuma ya kuvutar da su daga duk wani sharrin maqetaci, kamar dai yadda Xankutungayya da 'yan uwansa suka tsira daga Dodanniya. Haka kuma, tatsuniyar nan ta fassara mana karin maganar nan da ke cewa, mugunta fitsarin faqo ce, wanda ya yi ta take koma mawa.

 

 

Red Bouncing Right Arrow

Share & Interact!

Share Buttons

Follow Buttons

 

 

 

Join-the-discussion-at-BukarUsman-Forum.jpg
 

Forum5.jpg
Share a Folktale or a Response @

Have you read a book, story or an article of Bukar Usman's which you will like to comment about? Or, perhaps, YOU do have a folktale or a thought to share with others around the world? Or, maybe, you simply want to join the live discussion going on right now at the Bukar Usman online community forum? To be a contributor to this interesting forum, click the button below to navigate to the top-left corner of the Forum's home page, where you would be prompted to "Login" (for Dr Bukar Usman Forum members) or "Register" (for new guests). Join the talk!

 
Join-Forum.jpg
 

freedownload_70.jpg
Free Download
Access Dr Bukar Usman's folklore research, articles, reviews, and free book downloads, etc, by clicking the green button above.

Members-Only Download
membersgift.jpg
To be a special member of this site and receive Dr Usman's newsletter, his exciting contributions to folktales research, social insight, book previews, and news about the Dr Bukar Usman Foundation activities - and much more! - simply forward your main email address by filling in the form provided below. Click "Submit" to get the most exclusive resources sent to your email.

 

Your email address:

 

Shopping Cart, Rolling Wheel
Get Dr Usman's Books
Click the shopping cart above to buy Dr Bukar Usman's books.

Dankutungayya.gif
rana.jpg
TaskarTatsuniyoyi.gif

 
 

SandarArziki.gif

Littafin Sandar Arziki (Da Wasu Labarai) A Mahangar Nazari

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

 

Sunan Littafi: Sandar Arziki (Da Wasu Labarai).

Marubuci: Bukar Usman.

Mawallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano.

Shekarar Wallafa: 2005.

Yawan Shafuka: 65.

Farashi: Ba a faxa ba.

 

Littafin Sandar Arziki yana xauke ne da ingantattu kuma daxaxan tatsuniyoyi har guda tara, waxanda aka karkasa zuwa babi tara. Haka kuma, wannan littafi ya kasance xaya daga cikin jerin littattafai irinsa guda shida da ke qunshe a Taskar Tatsuniyoyi da Dokta Bukar Usman ya rubuta.

Daga shafi na 5 zuwa na 65, littafin na qunshe da waxannan tatsuniyoyi:  Tatsuniyar Sandar Arziki, tana xauke ne da labarin wani yaro mai ladabi da biyayya ga iyayensa, wanda haka ya sanya ya samu arziki da alherai masu yawa. Tatsuniyar na koya wa al'umma muhimmancin biyayya ga iyaye. Tatsuniya ta biyu ita ce ta Umbagila Da Dodo, inda wata yarinya ta kasance mai kunnen qashi, wacce ba ta jin maganar iyayenta, inda daga qarshe ta jawo wa kanta masifar auren dodo. Tatsuniyar na koya wa al'umma illar rashin bin maganar iyaye.

Tatsuniya ta uku kuwa, ita ce ta Makauniya Da Xanta, inda ake ba da labarin wata makauniya da xanta guda xaya, wacce ta raine shi cikin kulawa sosai. Tatsuniyar na koya mana muhimmancin gaskiya da riqon amana a vangare xaya, sannan kuma take koya mana illolin da ke tattare da hassada da ganin qyashi. Tatsuniya ta huxu kuwa, ta Sarkin Maqera Da Dodo, tana xauke da abubuwan mamaki da kuma ban tsoro. Tana koya mana muhimmancin jaruntaka, haquri da juriya. Tatsuniya ta biyar, wacce ta kasance 'Yar Mowa Da 'Yar Bora; tana ba da labarin wasu 'yan mata biyu ne 'yan gida xaya, inda kishiyar xaya ta riqa matsanta wa xaya yarinyar da ba xiyarta ba, ta maida ta bora, amma daga qarshe ta samu arziki mai yawa. Daga qarshe dai xiyarta, wacce take gatantawa, ta mayar da ita bora, amma ta samo tsiya da talauci. Tatsuniyar na nuna mana muhimmancin yi wa yara tarbiyya ta qwarai, kamar kuma yadda take gargaxinmu da kada mu aikata mugunta a rayuwa.

Tatsuniya ta shida mai suna Mai Haqar Vera, tana xauke ne da labarin wasu mafarauta, waxanda ke sana'ar farauta tare. Xaya daga cikinsu ya qi sauraren shawarar xaya, ya haqe wani rami, wanda ashe na kura ne, wacce daga qarshe ta halaka shi. Tatsuniyar na nuna mana illar taurin kai da rashin xaukar shawara da nasiha ta qwarai. Tatsuniyar Wata Mata Da Aljani ita ce ta bakwai a cikin wannan littafi. Tana ba da labarin wata mata ce da ta yi wa mijinta qarya, ta tsinto jariri a daji ta ce ita ta haife shi; inda daga qarshe suka gano ashe aljani ne ta tsinto kuma ya yi ta gallabarsu. Tatsuniyar na nuna mana illar qarya da ha'inci.

Tatsuniya ta takwas ita ce, Musare Da Hodanego, wacce kuma ke nuna mana muhimmancin kyakkyawar tarbiyya da amfanin tausayi da jinqai tsakanin al'umma. Tatsuniya ta tara kuma ta qarshe da ke cikin littafin nan ita ce ta Marayu Biyu. Tana ba da labarin wasu marayu ne wa da qanwa, waxanda suka rasa iyayensu, amma suka ci gaba da zama cikin kulawar juna. Tana koya mana muhimmancin yin gaskiya da kuma bin gaskiya a kowane lokaci, kamar kuma yadda take gargaxi ga masu aikata munafunci.

Babu shakka, littafin ya tsaru kuma marubucinsa ya zuba labarinsa cikin gwaninta da jan hankali; musamman kuma an qayata littafin da hotunan zane-zane masu qara armashi ga tatsuniyoyin.

Ko me ya ja hankalin Dokta Bukar Usman har ya rubuta wannan littafi?  Daga shafi na ix zuwa na xii, marubucin ya yi bayani dalla-dalla na dalilan da suka sanya ya yi wannan qoqari, inda yake cewa:

"Nakan tuno a lokacin da nake qarami, a kullum da dare bayan ni da sauran yara mun ci abinci, mahaifiyata kan yi mana tatsuniya a cikin harshen Babur/Bura a can garinmu Biu, na qasar Borno.

Idan da rani ne, mukan zauna a tsakar gida, wanda aka kewaye da zana. Wani lokacin kuma ga farin wata ya haske gari garau, kamar mutum ya tsinci allura a qasa; sararin sama kuma cike da taurari birjik, manya da qanana. Idan kuma da damina ne, sai mu zauna a cikin duhu a tsakar gidan, ko kuma a cikin xakin da aka hura wuta, musamman idan ana ruwa.

Tatsuniyoyin masu qayatarwa ne qwarai, kuma na ji daxinsu a lokacin. Waxansu tatsuniyoyin na ban tsoro ne, wasu kuwa akwai ban mamaki. Sai dai dukkaninsu suna buxe mana idanu da qara mana ilimin zaman duniya da dabarun zama da mutane.

Bayan haka, a lokacin da na fara karatun boko a wajen shekarar 1952, na karanta wasu littattafan Hausa kamar su Ka Koyi Karatu da Ruwan Bagaja da Magana Jari Ce da sauransu masu yawa, musamman waxanda shahararren marubucin nan, Alhaji Abubakar Imam ya rubuta. Kai bayan ma na yi murabus daga aikin Gwamnatin Tarayya a shekarar 1999, na ci gaba da karanta wasu littattafai da yawa da aka wallafa da Turanci, kamar na uwargidan Janar Domkat Bali, watau Esther Bali, wanda ya qunshi tatsuniyoyin mutanen Tarok da suke zaune a Jihar Filato da kuma waxanda wasu'yan Najeriya irinsu Shaihun malamin jami'a, Chinua Achebe da Cif Cyprian Ekwensi da Elechi Amadi suka rubuta. Bugu da qari, na karanta littattafai da yawa na shahararrun marubuta Turawa kamar su Chaucer da Shakespare da Jane Austin da Coleridge da Yeats. Duk waxannan littattafai sun sa na yi dogon tunani qwarai kan cewa ya kamata ni ma in rubuta littafin tatsuniyoyi da wasu labarai daga qasar Biu, watau mahaifata.

A wannan zamani, mutane da yawa sun san wasu littattafai da Turawa suka wallafa domin yaransu, kamar Tom and Jerry da Chalk Zone da Jimmy Newton da Mew Mew Power, waxanda har yaranmu ma sukan karanta su a namu makarantun, ko kuma su riqa kallonsu a talabijin ko ta faya-fayen bidiyo. Wannan ya nuna cewa akwai wajibci da buqata ga 'yan qasa su tashi tsaye su rubuta littattafai waxanda suka qunshi labarai irin namu, domin qara wa yaranmu ilimin da ya dace da qasarsu da yanayinta da xabi'un mutanenta, watau da misalan irin abubuwan da ke kewaye da mazauninsu.

Wani abin lura shi ne, ko labaran na 'yan Adam ne ko na aljanu ko na dabbobi, ko ma dai na wace irin halitta ne, suna nuni ne da halayya ta gari ko mummuna. Bugu da qari, akan ba da irin waxannan labarai ne domin a xebe kewa, kuma a koyar da darussan rayuwa masu amfani, kamar dai yadda na bayyana tun da farko. Don haka irin waxannan labarai suna da gindin zama a cikin adabi.

A cikin 'yan shekaru da suka shige ne na waiwayi waxannan tatsuniyoyi. Na je Biu musamman na yi bincike domin  in samo mutanen da suka san irin waxannan tatsuniyoyi na da. Na yi haka ne domin ganin yadda yawancin yaran yanzu kan fara karatun boko tun suna 'yan shekara uku a duniya, kuma idan sun koma gidajensu sai wasu su shiga kallon fina-finan bidiyo da talabijin, ko su sa waqoqin Makosa na mutanen qasar Kwango.

To, ina fata waxannan tatsuniyoyi za su rage haka, domin tun tuni gajerun labarai da tatsuniyoyi kan hana yara fita yawon banza kuma su zaunar da dattijai a gida cikin iyali.

A lokacin da nake bincike a kan tatsuniyoyin nan, na tuntuvi mutane da dama a qasar Biu, ciki har da wani da ya yi karatun boko har ya gama jami'a, amma ya ce bai tava jin ko xaya daga cikinsu ba. Wannan abu ya ba ni mamaki da qarfin gwiwar tattara tatsuniyoyin nan a cikin littafi, da fatan yara da manya za su amfana da su.

Wani abin lura kuma shi ne, manyanmu, watau tsofaffi, waxanda suka iya ba da waxannan tatsuniyoyi ba su da yawa kamar da, kuma sai raguwa suke ta yi. Sai na lura idan ba an rubuta waxannan tatsuniyoyi na adabin baka ba, ba shakka za su vace nan da 'yan shekaru kaxan masu zuwa. Allah Ya kiyaye faruwar haka, amin.

Duk da cewa akasarin tatsuniyoyin waxanda na ji ne a qasar Biu, na kawo su ne a cikin harshen Hausa saboda mutane da yawa su sami damar karanta su, kuma su kwatanta su da waxanda suka sani. Kowa ya san cewa yanzu Hausa ta zama harshen mutane daban-daban a Najeriya, har ma a qasashen waje. Shi ya sa ma na fara kowace tatsuniya da: Ga ta nan, ga ta nanku maimakon in fara da: Suk suku, watau yadda ake fara tatsuniya da harshen Babur/Bura, inda masu saurare kan amsa da: Sunta, watau an gayyace ka ka ba da labarin, kamar dai Ta zo mu ji ta a cikin harshen Hausa.

Ina fata jama'a za su samu qaruwa da wannan gudunmawa tawa."

Babu shakka wannan gudunmawa ta tabbata babban kavaki ga al'ummar yanzu da ma masu zuwa nan gaba. A yayin nazarin littafin nan, na ci karo da wasu 'yan kura-kurai, waxanda ya kamata a bugu na gaba a yi qoqarin gyara su. Kaxan daga cikinsu sun haxa da: A shafi na iv, an rubuta bashi maimakon ba shi. A shafi na v, an rubuta Haqan maimakon Haqar. A shafi na vii, an rubuta dukan su maimakon dukkansu. Shafi na ix, an rubuta shaharraren maimakon shahararren. Shafi na x, an rubuta jihar Pilatu maimakon Jihar Filato, sai kuma aka rubuta fayafayan maimakon faya-fayen. A shafi na xi kuwa, an rubuta 'yan adam maimakon 'yan Adam, sai kuma aka rubuta darusan maimakon darussan, a gaba kuma aka rubuta finafinan maimakon fina-finan. A shafi na xii, an rubuta Nigeria maimakon Najeriya.

Sauran kura-kuran sun haxa da: A shafi na xiv, an yi amfani da mawallafin maimakon marubucin. Shafi na xv an rubuta ko da yake maimakon kodayake, a gaba kuma aka rubuta gwamaya maimakon gwamutsa. Duk dai a wannan shafin, an rubuta maqwafin maimakon makwafin. Sai kuma shafi na xvii, inda aka rubuta yakamata maimakon ya kamata. A shafi na 6, an rubuta jifan maimakon jifar, sandana maimakon sandata. A shafi na 7, aka rubuta Yakan maimakon Takan. A shafi na 12, an rubuta xiban maimakon xibar. Shafi na 19, an rubuta bukatu maimakon buqatu. Haka kuma, a shafi na 39, an rubuta jimlar qwai da qwaiqwaye maimakon qwayaye. A shafi na 43, an rubuta kaiwa maimakon kai wa. Sai kuma shafi na 44, inda aka rubuta farautansa maimakon farautarsa. A shafi na 56 kuwa an rubuta hanunta maimakon hannunta. Sai kuma a shafi na 63 da aka rubuta tacinye maimakon ta cinye. Duk da cewa waxannan kura-kurai sun bayyana, amma ba su gurvata ma'anonin da ake nufi ba kuma ba su taka kara sun karya ba. 

Babu shakka littafin nan zai zama abokin hira ga yara da manya, kamar kuma yadda zai koyar da darussa masu yawa. Ina fata al'umma za su mallaki littafin nan, domin kuwa taska ce babba, abin adanawa. Haka kuma, ina kira ga makarantu da cibiyoyin ilimi da su tanadi littafin nan, domin kuwa zai fa'idantar.

 
   

©bukarusman.com 2017  All rights reserved.

Powered by  Nakolisahost.com