Home | English | Hausa | Books | Reviews | Readers | News | Articles | Awards | About | Contact | Download | Audio/Video

Littattafai

mudplaster-house.gif
savannah.jpg
mud-house_115.gif
people_120.jpg
books2_150.jpg

Tatsuniyoyi
Tsokaci
Biu

Daga Ashafa Murnai Barkiya, a Abuja

Bayan Ya Kammala Gina Wa Hausa Taskoki 14

Dakta Bukar Usman Ya Fara Shirin Korar ‘Tom And Jerry A {asar Hausa

A satin da ya gabata kun karanta ta}aitattun bayanan da littattafan nan Taskar Tatsuniyoyi su ka }unsa, wa]anda hazi}in mai kishin Hausa Dakta Bukar Usman ya rubuta. to litattafan nasa ba na [aya zuwa na Shida ba ne ka]ai. Dakta Bukar ashe ya }ara maleji inda a halin yanzu ya kammala sauran taskokin inda sun kai goma sha hu]u. Babu abin da ya rage ga Hausawa sai kawai su yi tururuwa su na shiga taskokin su ci albarkacin ]an }abilar Babur.

Bukar Usman ya shaida wa LEADERSHIP HAUSA cewa a yanzu haka aiki ya kankama inda za a maida wa]annan litattafai 14 a matsayin tatsuniyoyin da za a ri}a kallo a cikin talbijin ta hanyar warware su a fayafayen CD. A ta}aice dai wata hikima ce Dakta Bukar ya shigo da ita doin hana yaran Hasawa kallon Tom and Jerry. Lallai sau}i ya samu domin nan ba da da]ewa ba za mu ri}a ganin su Gizo da {o}i da sauran dodannin cikin tatsuniyoyi su na magana da Hausa. Ya rage ga Hausawa su tashi tsaye su kar~i wannan yin}uri da hannu bibbiyu.

Yanzu dai a jimlace litattafan Dakta Bukar Usman 14 na tsakar Tatsuniyoyi su ne:

Littafi Na [aya: Marainiya

Littafi Na Biyu: Jarumin Sarki

Littafi Na Uku: Yarima Da Labbi

Littafi Na Hu]u: Tsurondi

Littafi Na Biyar: Sandar Arziki

Littafi Na Shida: [ankutungayya

Littafi Na Bakwai: Gwaidayara

Littafi Na Takwas: [an Agwai Da Kura

Littafi Na Tara: Tsohuwa Da 'Yan Mata Uku

Littafi Na Goma: [ankucaka

Littafi Na Sha [aya: Al'ajabi

Littafi Na Sha Biyu: 'Yargata

Littafi Na Uku: Duguli [an Bajinta

Littafi Na Sha Hu]u: Muguwar Kishiya.

Ga ka]an daga cikin abubuwan da ke cikin littafi na 7 zuwa na 14:

A cikin wannan littafi mai suna Gwaidayara an yi amfani da mutane da wasu namun daji da }wari da tsuntsaye. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi tara ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi ta }unshi yadda ake so mutum ya zama mai kyautata wa jama'a da yi musu alheri da muhimmancin girmama bako, sannan an nuna muddin ka shuka alheri shi za ka girba a rayuwarka.

A cikin littafi na Takwas: A cikin wannan littafi mai suna [an Agwai an yi amfani da mutane da wasu namun daji da }wari da tsuntusaye. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma sha ]aya ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi tana nuna mana yadda ya kamata ]an'Adam ya ri}a tausayi da kuma jin}an mutane da kuma dabbobi a matsayinsu na halittun Allah, domin yin hakan ya kan kawo babban alheri ga rayuwar duk mai aikata hakan.

Littafi na Tara: A cikin wannan littafi mai suna Tsohuwa Da 'Yan Mata Uku, an yi amfani da mutane da wasu namun daji. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoy goma sha uku ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi tana nuna mana yadda taimakon Allah yake riskar ]an'Adam ba zato ba tsammani, sannan kuma idan mutum ya yi maka mummunan abu a rayuwa, to kai ka yi masa mai kyau, yin hakan zai sa mutumin ya gane kurensa, har ya yi nadama da ga baya kuma ya sauya halinsa.

Littafi na Goma: A cikin wannan littafi mai suna [ankucaka an yi amfani da mutane da wasu namun daji da }wari da tsuntusaye. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma sha biyu ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi ta nuna mana yadda illolin yin }arya suke a rayuwa, sannan kuma yaudara ba ta da amfani, haka zalika an nuna cewa kayan aro ba su rufe katara. Abu mafi kyau shi ne kowa ya tashi ya nemi abun kansa.

Littafi na Sha [aya: A cikin wannan littafi mai suna Al'ajabi an yi amfani da wasu namun daji da }wari da tsuntsaye. Litafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma ne, kowace da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi tana nuna mana yadda ake so mutum idan an gaya masa wata magana ya yi bincike kafin ya yarda da ita ko kuma zartar da hukunci a kan abin da ya ji, domin ]aukar kowacce irin magana ba tare da bincikawa ba, kan jawo da-na-sani. Wannan kuma ya dace da kalaman masu iya magana da ke cewa: "In mafa]in magana wawa ne, to majiyinta kada ya zama wawa."

Littafi na Sha Biyu: A cikin wannan littafi mai suna 'Yargata an yi amfani da mutane da wasu namun daji da }wari da tsuntsaye. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi tana nuna mana yadda ake so mutum ya zama mai }as}antar da kai ban da yin ]agawa da nuna ka fi kowa, kowane irin matsayi ko ilimi kake da shi, domin duk iliminka ko matsayinka akwai wanda ya fi ka, cikinsu kuwa har da mahaifa da malamanka ko wa]anda suka raine ka a fannin da ka yi fice.

Littafi na Sha Uku: A cikin wannan littafi mai suna Duguli [an Bajinta an yi amfani da mutane da wasu namun daji da dabbobin gida da }wari da dodanni da wasu hanyoyi na siddabaru. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

[aya daga cikin wa]annan tatsuniyoyi ta }unshi labarin wani maharbi ne mai wata 'ya kyakkyawa. Saboda tsananin kyanta ba ya bari kowa ya ganta. Wata rana sanda babanta ba ya nan ta le}o }ofar gida, sai wani mutum ya ganta, ya garzaya ya tsegunta wa sarkin garin. Da sarki ya yi hawa don ya gane wa idonsa sai ya tarar da gidan a kulle, amma ya sa aka karya }ofar aka shiga aka fito da yarinyar, ta kuma tsuma shi sai ya tafi d aita a matsayin matarsa.

Da ta tare sai sarki ya garga]i matansa kan cewa kada wata ta sa ta aiki. Rannan sarki ba ya nan sai kishioyinta suka tilasta mata sai ta yi aiki. To, tana farawa kuwa sai ska ga ta riki]a ta zama }wallon dabino, suka kuwa ]auki }wallon suka wurga shi a kogi. Daga nan sai bishiyar dabino ta tsiro, ta girma, sai aka hango amarya a kanta. Da sarki ya dawo ya ji abin da ya faru sai ya sa aka dawo da ita gida. Saboda wannan laifi da matansa suka aikata sai ya sa aka fiffile musu kawuna har da na wasu 'ya'yansa. ance : "Munafunci dodo ne yakan ci mai shi."

Littafi na Sha Hu]u: A cikin wannan littafi mai suna Muguwar Kishiya an yi amfani da mutane da wasu namun daji da dabbobin gida da }wari da Gizo da {o}i. Littafin kuma ya }unshi tatsuniyoyi goma sha ]aya ne, kowacce da irin abin da take koyarwa.

Hu]u daga cikin tatsuniyoyin sun shafi munanan halaye na zaman kishiya. Misali, akwai wani mutum mai mata biyu. Na ]aya ita ce uwargida. Tana da 'ya'ya da yawa. Na biyu ita ce amarya. Ita Allah ya ba ta 'ya mace ]aya tak.

Amaryar ta kamu da rashin lafiya wand aya zama sanadin mutuwarta. Amma kafin ta mutu sai da ta bar wa kishiyar amanar 'yarta. Bayan mutuwarta sai uwargida ta tsani 'yar amarya har ma tana hana ta abinci.

Wata rana mijinsu ya je kasuwa ya sayo wa 'ya'yansa tsaraba har da }osai wanda 'yar amarya ta nemi ya sayo mata. Ta shuka wannan }osan ya tsiro ya zama bishiya. 'ya'yan bishiyar ne suka zama abincinta. Duk sanda take bu}atar abinci sai ta yi wa}a 'ya'yan itancen su fa]o sai ta ]iba ta ci.

Da kishiyar uwar da 'ya'yanta suka so su ci }osan ba su yi nasara ba, sai ta }ulla makircin hallaka 'yar amarya ta hanyar saka mata guba cikin kunu. Amma 'yar amarya ba ta sha ba saboda bishiyar ta sanar da ita wannan makircin, sai 'ya'yanta ne suka sha kunun, suka kuma mutu gaba ]ayansu; uwarsu kuma ta kma kuka tana da-na-sani. An ce: "In za ka ha}a ramin mugunta, ha}a shi gajere."

 

*Leadership Hausa, 12 - 18, Ga Maris, 2010

 

 

 

   

BU_in_trad_attire.JPG

Dakta Bukar Usman

 
Click the image below to read reviews
of Dr Bukar Usman's Hausa books
 
 
Bookreviewicon1.jpeg
 

 
Click the image below to read
 
 
Bookreview2.jpeg
 

Marainiya.gif

Littafi Na Daya

JaruminSarki.gif

Littafi Na Biyu

YarimaDaLabbi.gif

Littafi Na Uku

Red Bouncing Right Arrow

Share & Interact!

Share Buttons

Follow Buttons

 

 

 

Join-the-discussion-at-BukarUsman-Forum.jpg
 

Forum5.jpg
Share a Folktale or a Response @

Have you read a book, story or an article of Bukar Usman's which you will like to comment about? Or, perhaps, YOU do have a folktale or a thought to share with others around the world? Or, maybe, you simply want to join the live discussion going on right now at the Bukar Usman online community forum? To be a contributor to this interesting forum, click the button below to navigate to the top-left corner of the Forum's home page, where you would be prompted to "Login" (for Dr Bukar Usman Forum members) or "Register" (for new guests). Join the talk!

 
Join-Forum.jpg
 

freedownload_70.jpg
Free Download
Access Dr Bukar Usman's folklore research, articles, reviews, and free book downloads, etc, by clicking the green button above.

Members-Only Download
membersgift.jpg
To be a special member of this site and receive Dr Usman's newsletter, his exciting contributions to folktales research, social insight, book previews, and news about the Dr Bukar Usman Foundation activities - and much more! - simply forward your main email address by filling in the form provided below. Click "Submit" to get the most exclusive resources sent to your email.

 

Your email address:

 

Shopping Cart, Rolling Wheel
Get Dr Usman's Books
Click the shopping cart above to buy Dr Bukar Usman's books and other good reads from around the world being offered by his publishers. There's a special section for those paying in Naira. It's 100%-secure shopping!

Shopping Cart, Rolling Wheel
Get Dr Usman's Books
Click the shopping cart above to buy Dr Bukar Usman's books.

©bukarusman.com 2017  All rights reserved.

Powered by  Nakolisahost.com