Home | English | Hausa | Books | Reviews | Readers | News | Articles | Awards | About | Contact | Download | Audio/Video

Tatsuniyoyi
Tsokaci
Biu

Littattafan Tatsuniyoyin Na Dakta Bukar Usman: *Taskar Tatsuniyoyi: Littafi Na Daya Zuwa Na Goma Sha Hudu *Alajabi *Dan Agwai Da Kura *Dankucaka *Dankutungayya *Duguli Dan Bajinta *Gwaidayara *Jarumin Sarki *Marainiya *Muguwar Kishiya *Sandar Arziki *Tsohuwa Dan Yan Mata Uku *Tsurondi *Yargata *Yarima Da Labbi

Dokta Abubakar Imam malamina ne - Marubuci Bukar Usman
 
 
                 By Bashir Yahuza Malumfashi
 
 

ImamAwardPhotoH.jpg

Dokta Bukar Usman OON, marubucin babban kundin Taskar Tatsuniyoyi na xaya daga cikin fitattun marubutan da aka karrama a Bikin Tunawa Da Abubakar Imam, wanda ya gudana a Asabar da ta gataba. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana cewa marigayi Imam malaminsa ne, kuma ga yadda tattaunawar ta kasance:

Kana xaya daga cikin fitattun marubuta da qungiyar Alqalam ke karramawa a yau, domin tunawa da marigayi Abubakar Imam; me za ka ce game da wannan al'amari?

Wannan babbar rana ce kuma zan iya cewa shi marigayi Dokta Abubakar Imam, ni xalibinsa ne. Duk da cewa ban tava haxuwa da shi fuska-da-fuska ba a rayuwa, amma tun a shekerar 1951, lokacin da na shiga firamare, da littattafansa muka fara koyon karatun Hausa. Tun daga lokacin nan, babu wani malamin Hausa da ya koyar da ni Hausa. Dalili ke nan na ce ni xalibinsa ne, duk da cewa bai koyar da ni ba a cikin aji, amma dai littattafansa ne suka yi mani jagora ga karatu da rubutun Hausa. Wannan ta kai ga cewa har a yau ina rubuta littattafai, wasu cikin Ingilishi, wasu kuma cikin harshen Hausa. Kuma cikin ikon Allah, sai ga shi a yau littattafan da na rubuta da Hausa sun fi yawa. Saboda haka, a yau da aka ware domin bikin tunawa da shi, ai babbar rana ce a gare mu da kowa ma da yake alfahari da harshen Hausa. Don haka, sai dai mu ce alhamdu lillahi.

Mutane da dama suna mamakin yadda ka juya alqalaminka zuwa rubuce-rubuce da harshen Hausa, duk kuwa da cewa kai ba Bahaushe ba ne. Me ya ba ka sha'awar xaukar wannan mataki, ga shi ma har ka yi zarra a rubuce-rubucen Hausa?

Lokacin da na fara rubuta littafin tarihin rayuwata da Ingilishi, sannan na rubuta wani littafin wanda ya shafi harkokin aikin gwamnati, mutumin da ya yi mani aikin xab'insu sai ya ce mani: ‘Ga shi ka gama waxannan littattafai, babu wani abu kuma?' Na tambaye shi cewa, kamar waxanne irin abu kuma? Sai ya ce mani kamar abubuwan da suka shafi al'umma. Ni kuma sai na tuno da tatsuniyoyi da almara, don haka sai na maida hankali a kansu. Shi ya sanya ma mafi yawan littattafan da na rubuta da Hausa, sun danganci tatsuniyoyi da almara ne. Wani ya qalubalance ni cewa, me ya sanya ban rubuta littattafan cikin harshena na Babur ba, sai na ce masa saboda ina son saqonnin da ke qunshe cikinsu su isa zuwa ga mutane da yawa, ba ga al'ummar Babur kaxai ba. Na sanar da shi cewa masu amfani da harshena ba su da yawa, domin Hausa ya zama babban harshen da ya zama gama-gari, ya zama harshen kasuwanci kusan ma yana nema ya zama harshen duniya. A nan Najeriya, an yi ta tattaunawa, cewa wane yare ne zai yi saurin mutuwa? Aka ce harshen Ibo, bayansa sai na Yarabanci, sannan na Hausa, domin shi na Hausa ana wallafa littattafai da yawa da shi kuma ana karantawa sosai. Haka kuma ta kafafen watsa labarai, ana amfani da shi. Amma ba ka jin suna amfani da wasu yarukan da dama da ake da su. Za ka samu sashen Hausa a manyan gidajen rediyo kamar BBC, Rediyo Dutche Welle, Rediyo Faransa, kai har a Yamai, Jamhuriyar Nijar, akwai gidajen rediyo da ke amfani da harshen Hausa wajen watsa shirye-shiryensu. Ga wasu gidajen rediyon a Ghana da Muryar Amurka da Rediyo China, duk za ka ji suna watsa shirye-shiryen Hausa.

Su waxannan littattafai na Taskar Tatsuniyoyi da ka wallafa, wasu masana na ganin cewa yadda zamani ya sauya, akwai buqatar a mayar da su zuwa fina-finai, koda na zane-zane (cartoon) ne. Ko akwai wani qoqari da kake yi ta wannan fuska?

Wannan gaskiya ne, domin kuwa muna qoqari ta wannan fuska. Mun lura da yadda irin waxannan fina-finai na Tom & Jerry ke xaukar hankalin al'umma, musamman ma yadda yaranmu ke da nacin kallonsu. Daloli ke nan muka fara bincike a nan Najeriya, domin neman wanda zai iya juya tatsuniyoyin namu zuwa zane-zane masu motsi irin na Tom & Jerry amma har yau ba mu samu ba. Amma dai muna ci gaba da bincike, idan muka samu za a yi. Haka ma lokacin da muka je Yamai a Jamhuriyar Nijar, mun tambaya ko akwai mai zane da zai iya yin waxannan zane? An sanar da ni cewa akwai amma dai har yanzu babu wanda ya ce ga shi zai yi. Amma dai na san ba da daxewa ba, nan gaba za a samu damar yi.

Idan muka dawo kan batun marigayi Abubakar Imam, wanda ake karramawa a yau xin nan, ko akwai wani kira ko jan hankali da za ka yi ga gwamnati, domin bunqasa ayyukansa, domin al'ummar baya ita ma ta amfana?

Na ga ayyukansa da rubuce-rubucensa da kayayyakinsa, shi ne na gaya wa xansa Najimuddeen Imam da kuma Uban Qungiyar Alqalam, Mahmoon Baba Ahmad, cewa waxannan littattafai nasa da tarihinsa, ya kamata a adana su sosai a gidan tarihi. Na tava zuwa qasar Jamaica, na ziyarci gidan mawaqin nan Bob Merly. Gidan ya zama gidan tarihi, duk baqon da zai shiga sai ya biya kuxi da Dala kafin ya shiga domin ganin kayan tarihinsa, kamar gadon kwanciyarsa da sauransu. Kai har ma da xaurin wiwi, an ajiye a wani wuri, wacce za ta nuna maka alamar cewa ya yi mu'amala da wannan taba. Akwai kuma wani vangaren, gidan sinima ne, wanda ke nuna wasanninsa da waqoqinsa. Ga tarihinsa, ga abubuwan da ya rayu yana aikatawa da sauransu, wurin ya zama wurin ziyarar baqi domin shaqatawa. Don haka, shawararar da na ba su Mahmoon ke nan, cewa a yi qoqarin yin gidan tarihi na Abubakar Imam kuma su samu masanin harkar laburare qwararre, yadda za a tsara da adana waxannan ayyuka nasa a zamanance.

Ka kafa Gidauniyar Bukar Usman, ko akwai wata gudunmowa da take bayarwa domin bunqasa irin waxannan ayyuka na adana tarihin marubuta da sauransu?

Muna yi, domin muna ba da tallafi ga marubuta, musamman idan mutum ya yi rubutun littafin da zai amfani al'umma amma bai da yadda zai wallafa shi, daidai gwargwado muna ba da tallafi amma ba wai xaukar nauyi duka ba. Kuma ita gidauniyar, ba ta tsaya kaxai wajen tallafin harkar rubutu kaxai ba. Muna taimakawa wajen tallafi ga marasa lafiya da sauran lalurori da suka addabi marasa galihu. Ya danganta da lalurar da aka gabatar zuwa gare mu kuma idan mun ga da hali, sai mu taimaka daidai gwargwado.

A wasu vangaren, marubuta da suka yi fice za ka ga an sanya gasar rubutu ko makamancin haka, inda duk shekara za a riqa ba da kambi ga wanda ya ci gasar da sunansu, misali kamar Wole Soyinka da Chinua Achebe, ko kana ganin ya dace a fito da irin wannan gasa da sunan tunawa da Abubakar Imam?

Kamar dai yadda wannan qungiya ta Alqalam ta yi, ta tara babban taro irin wannan ta karrama mu domin tunawa da shi, ka ga ba gasa suka sanya ba, sun dai yi la'akari da wata gudunmowa da muke bayarwa ga al'umma. Idan aka ce an sanya gasa, abin zai qarfafa wa marubuta gwiwa a wannan zamani.

Ko akwai wani qarin bayani daga gare ka, dangane da wannan taro na tunawa da marigayi Dokta Abubakar Imam?

Wannan shi ne na fari kuma yadda aka shirya shi a nan Gidan Arewa, kuma a nan inda muke tattaunawar nan, ga gidan Firimiya Sardauna Ahmadu Bello nan muna gani, inda ainahin gidansa ke nan lokacin da yake raye. Ga shi dai muna ganin xakinsa wanda qarami ne, ba irin manya-manyan gine-ginen da ake yi a wannan zamani ba ne, amma dai ga shi nan yana tsaye. Wannan babban darasi ne ga al'ummarmu kuma Gidan Arewa sun yi qoqari sosai da suka samar da wannan gida na tarihi da adana al'adun manyanmu na jiya. Don haka baya ga wannan karramawa da aka yi mana kuma mun yi farin ciki da wannan gida na tarihi a yau.

__________________________________________________________________________________

An buga wannan hira a jaridar Aminiya ta Juma'a 10 ga watan Maris, 2017, shafi na 33

©bukarusman.com 2017  All rights reserved.

Powered by  Nakolisahost.com